1 Chronicles 10:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da dukan Isra’ilawa a cikin kwari suka ga cewa mayaƙansu suna gudu, kuma cewa Shawulu da ’ya’yansa maza sun mutu, sai suka bar garuruwansu suka gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka zauna a cikinsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ دَسُكٜىٰ ذَمَ أَ ݣُورِنْ يٜىٰظِرٜىٰيٜىٰلْ سُكَغَ سُواْجُواْجِنْ سُنَ غُدُ كُمَ سُكَجِ ثٜىٰوَ طَالُوتَ دَ یَیَنْسَ سُنْ مُتُ، سَيْ سُو مَا سُكَ غُدُ سُكَ بَرْ غَرُرُوَنْسُ؞ ڢِلِسْتِيَاوَا كُوَ سُكَذُواْ سُكَ ذَوْنَ أَوُرِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da dukan Isra'ilawa waɗanda suke zaune a kwari suka ga sojojin sun gudu, Saul kuma da 'ya'yansa maza sun mutu, sai suka bar garuruwansu suka gudu. Filistiyawa suka zo suka zauna a wurin.