1 Chronicles 10:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka tuttuɓe shi suka yanke kansa suka ɗauka duk da kayan yaƙinsa, suka kuma aika ’yan aika ko’ina a ƙasar Filistiyawa, a yi shela labarin a cikin gumakansu da kuma mutanensu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سُكَ يَنْكٜىٰ كَنْ طَالُوتَ، سُكَ طَوْكِ كَنْسَ دَ كَايَنْ يَاڧِنْسَ، سُكَ عَيْكَ دَ یَنْ سَڧُواْ ذُوَا كُواْعِنَ عَڧَسَرْ ڢِلِسْتِيَاوَا سُكَيْ لَابَرِ مَيْ دَاطِے غَ مُتَنٜىٰنْسُ سُكُمَ غُواْدٜىٰ وَغُمَكَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suka kuwa tuɓe tufafinsa, suka datse kansa suka ɗauka duk da kayan yaƙinsa, suka aiki manzanni ko'ina a ƙasar Filistiyawa don su ba gumakansu da jama'arsu wannan albishir.