1 Chronicles 11:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A dā, ko a lokacin da Shawulu yake sarki, ai, kai ne kake shugabantar Isra’ila a yaƙe-yaƙe. Kuma Ubangiji Allahnka ya ce maka, ‘Za ka zama makiyayin mutanena Isra’ila, za ka kuma zama mai mulkinsu.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تُنْ لُواْكَثِنْ دَ طَالُوتَ يَكٜىٰ سَرْكِنْمُ، كَيْنٜىٰ كَكٜىٰبِے دَ إِسْرَٰٓءِيلَ عَيَاڧِ؞ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكَ كُمَ يَغَيَ مَكَ ثٜىٰوَ كَيْنٜىٰ ذَاكَ ذَمَ مَكِيَايِنْ مُتَنٜىٰنْسَ إِسْرَٰٓءِيلَ، ذَاكَ كُمَ ذَمَ سَرْكِنْسُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ko dā can lokacin da Saul yake sarauta, kai ne kake yi wa Isra'ilawa jagora zuwa yaƙi da komowa. Ubangiji Allahnka kuwa ya ce maka, ‘Za ka yi kiwon jama'ata, wato Isra'ilawa, ka kuma shugabance su.’ ”