1 Chronicles 11:26 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Jarumawan nan su ne, Asahel ɗan’uwan Yowab, Elhanan ɗan Dodo daga Betlehem,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا سُونَيٜىٰنْ سُواْجُواْجِنَّنْ مَڢِيَ عِيَ يَاڧِ سُواْسَيْ، أَسَهٜىٰلْ طَنْعُوَنْ يُواْوَبْ، عٜىٰلْهَنَنْ طَنْ دُواْدُواْ مُتُمِنْ بَيْتَلَحْمِ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗannan su ne manyan jarumawan sojoji. Asahel ɗan'uwan Yowab Elhanan ɗan Dodo daga Baitalami Shamma daga Harod Helez daga Felet Aira ɗan Ikkesha daga Tekowa Abiyezer daga Anatot Sibbekai daga Husha Ilai daga Aho Maharai daga Netofa Heled ɗan Ba'ana daga Netofa Ittayi ɗan Ribai daga Gibeya ta Biliyaminu Benaiya na Firaton Hurai daga rafuffuka kusa da Ga'ash Abiyel daga Araba Azmawet daga Bahurim Eliyaba daga Shalim 'Ya'yan Yashen, maza, daga Gizon Jonatan ɗan Shimeya daga Harod Ahiyam ɗan Sharar daga Harod Elifelet ɗan Ahasbai Hefer daga Mekara Ahaija daga Felet Hezro daga Karmel Nayarai ɗan Ezbai Yowel ɗan'uwan Natan Mibhar ɗan Hagri Zelek daga Ammon Naharai daga Biyerot (Mai riƙe wa Yowab ɗan Zeruya makamai) Aira da Gareb daga Yattir Uriya Bahitte Zabad ɗan Alai Adina ɗan Shiza (Shi ne shugaba a kabilar Ra'ubainu, yana da ƙungiyarsa mai soja talatin tare da shi) Hanan ɗan Ma'aka Yoshafat daga Mitna Uzziya daga Ashtera Shama da Yehiyel 'ya'yan Hotam, maza, daga Arower Yediyel da Yoha 'ya'yan Shimri, maza, daga Tiz Eliyel daga Mahawa Yeribai, da Yoshawiya 'ya'yan Elna'am, maza Itma daga Mowab Eliyel, da Obida, da Yawasiyel daga Zoba,