1 Chronicles 11:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka zo wurin Sarki Dawuda a Hebron, suka yi yarjejjeniya da shi a gaban Ubangiji, suka kuwa shafe Dawuda ya zama sarki a bisa Isra’ila, yadda Ubangiji ya yi alkawari ta wurin Sama’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ دُكَنْ دَتَّاوَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَذُواْ وُرِنْ سَرْكِے دَاوُدَ أَ هٜىٰبْرُوانْ، سَيْ سَرْكِے يَيِ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ دَسُو أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ سُكَ كُمَ ظُبَ وَ دَاوُدَ مَنْ كٜىٰٻٜىٰوَ دُواْمِنْ يَذَمَ سَرْكِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ بِسَغَ مَغَنَرْ يَهْوٜىٰهْ تَبَاكِنْ سَمَٰعِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai dattawan Isra'ilawa suka zo wurin sarki Dawuda a Hebron. Dawuda kuwa ya yi alkawari da su a Hebron a gaban Ubangiji, ake kuwa naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra'ila bisa ga faɗar Ubangiji ta bakin Sama'ila.