1 Chronicles 12:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Dawuda ya fita don yă tarye su, ya kuma ce musu, “In kun zo wurina da salama, don ku taimake ni, to, ina a shirye in bar ku ku haɗa kai tare da ni. Amma in kun zo don ku bashe ni ga abokan gābana sa’ad da hannuwana ba su da laifi a rikici, bari Allah na kakanninmu yă duba yă kuma shari’anta ku.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ دَاوُدَ يَڢِتُواْ دُواْمِنْ يَتَرْيٜىٰسُ؞ يَثٜىٰ مُسُ «عِدَنْ كُكَ ذُواْ وُرِينَ ثِكِنْ أَلْحٜىٰرِ دُواْمِنْ كُتَيْمَكٜىٰنِ، نِے نَا كَرْٻٜىٰكُ؞ عَمَّا عِدَنْ كُنْ ذُواْ كُبَاشٜىٰنِ غَ أَبُواْكَنْ غَابَنَ نٜىٰ، نِے كُوَ بَنْ يِمُكُ لَيْڢِے بَ، اللَّهْ نَكَاكَنِّنْمُ ذَيْ غَنِ، ذَيْ كُوَ يِمُكُ شَرِيعَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Dawuda ya fito don ya tarye su, ya ce musu, “Idan da salama kuka zo wurina don ku taimake ni, to, zuciyata za ta zama ɗaya da taku, amma idan kun zo ne don ku bashe ni ga maƙiyana, to, Allah na kakanninmu ya duba ya shara'anta, da yake ba ni da laifi.”