1 Chronicles 12:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai waɗansu mutanen Gad suka koma suna goyon bayan Dawuda suka kuma haɗa kai da shi a kagararsa a hamada. Su ƙwararrun mayaƙa ne, a shirye don yaƙi, kuma suna iya riƙe garkuwa da māshi. Fuskokinsu kamar fuskoki zakoki, kuma suna da sauri kamar bareyi a kan duwatsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَغَ ذُرِيَرْ غَدْ أَݣَويْ وَطَنْسُ دَ سُكَبِے دَاوُدَ ذُوَا وُرِنْ ٻُيَنْسَ أَدَاجِ؞ سُو ڠُونَيٜىٰنْ يَاڧِنٜىٰ، كُمَ مَاسُ عِيَ يَاڧِ دَ غَرْكُوَ دَ مَاشِ؞ سُنَ رِڧٜىٰ دَ ڢُسْكُواْكِ كَمَرْ ذَاكِ، سُنَ كُمَ غُدُ عَكَنْ دُوَڟُو كَمَرْ بَرٜىٰوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗannan su ne sunayen shahararru, ƙwararrun mayaƙa daga kabilar Gad, waɗanda suka haɗa kai da sojojin Dawuda, sa'ad da yake a kagara a hamada. Su gwanayen yaƙi da garkuwa da mashi ne. Fuskokinsu kamar na zakoki, saurinsu kamar bareyi a kan dutse.