1 Chronicles 13:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Akwatin Alkawarin Allah ya zauna tare da iyalin Obed-Edom a gidansa wata uku, Ubangiji kuwa ya albarkaci gidan Obed-Edom da kome da yake da shi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَݣُوتِنْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَرْ اللَّهْ يَذَوْنَ أَغِدَنْ عُواْبٜىٰدْ عٜىٰدُوامْ مُتُمِنْ غَتْ وَتَا عُكُ؞ يَهْوٜىٰهْ كُوَ يَ أَلْبَرْكَثِ عِيَلِنْ عُواْبٜىٰدْ عٜىٰدُوامْ دَ دُكَنْ أَبِنْدَ يَكٜىٰدَشِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Akwatin alkawarin Allah kuwa ya kasance a gidan Obed-edom har wata uku. Ubangiji kuwa ya sa wa iyalin Obed-edom da dukan abin da yake da shi albarka.