1 Chronicles 13:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dawuda da dukan Isra’ilawa tare da shi suka tafi Ba’ala na Yahuda (Kiriyat Yeyarim) don su haura daga can su kawo akwatin alkawarin Allah Ubangiji, wanda yake zama tsakanin kerubobi, akwatin alkawarin da ake kira da Sunan.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ دَاوُدَ يَتَڢِے بَعَلَ، وَتُواْ كِرِيَتْ يٜىٰيَرِمْ، عَڧَسَرْ يَهُودَ، يَتَڢِے دَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ دَسُكٜىٰ تَرٜىٰ دَشِ دُواْمِنْ سُكَٰوُاْ عَݣُوتِنْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَرْ اللَّهْ ، وَدَّ عَكٜىٰ كِرَنْتَ دَ سُونَنْ يَهْوٜىٰهْ ، يَهْوٜىٰهْ وَنْدَ يَكٜىٰ ذَمَ بِسَنْ حَلِتُّو مَاسُ ڢِكَڢِكَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Dawuda tare da dukan Isra'ilawa, suka haura zuwa Ba'al, wato Kiriyat-yeyarim ta Yahuza, domin su ɗauko akwatin alkawarin Allah daga can, inda ake kira bisa sunan Ubangiji, wanda kuma yake zaune a wurin kerubobi.