1 Chronicles 14:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da Filistiyawa suka ji an naɗa Dawuda sarki a bisa dukan Isra’ila, sai suka haura da cikakken mayaƙa don su neme shi, amma Dawuda ya ji game da wannan ya kuwa fita don yă ƙara da su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ ڢِلِسْتِيَاوَا سُكَجِ أَنَّطَ دَاوُدَ سَرْكِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ، سَيْ دُكَنْسُ سُكَڢِتَ نٜىٰمَنْسَ دُواْمِنْ سُكَامَ شِ؞ دَ دَاوُدَ يَجِ حَكَ سَيْ يَڢِتَ دُواْمِنْ يَسَدُ دَسُو؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da Filistiyawa suka ji an naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra'ila duka, sai dukan Filistiyawa suka haura, suna neman Dawuda. Da Dawuda ya ji labari, sai ya fita domin ya yi yaƙi da su.