1 Chronicles 15:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Domin ku, Lawiyawa ba ku haura da shi da farko ba ne ya sa Ubangiji Allahnmu ya husata a kanmu. Ba mu tambaye shi game da yadda za mu yi shi a hanyar da aka ƙayyade ba.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ بَكُو نٜىٰ كُكَ طَوْكٜىٰشِ دَ ڢَرْكُواْ بَ، سَيْ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْمُ يَٻَرْكٜىٰ دَ ڢُشِنْسَ عَكَنْمُ، تُنْدَيَكٜىٰ بَمُ طَوْكِ عَݣُوتِنْ بِسَغَ ڧَٰعِدَرْسَبَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama Ubangiji Allahnmu ya fashe fushinsa a kanmu saboda ba ku ne kuka ɗauke shi a karo na farko ba, saboda kuma ba mu yi masa sujada kamar yadda aka umarta ba.”