1 Chronicles 15:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Dawuda da dattawan Isra’ila da shugabannin ƙungiyoyi dubu suka haura don su kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga gidan Obed-Edom, da farin ciki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ دَاوُدَ دَ دَتَّاوَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ مَنْيَنْ شُوغَبَنِّنْ سُواْجُواْجِنْ دَسُكٜىٰ مُلْكِ عَكَنْ سُواْجُواْجِ دُبُو دُبُو، سُكَ تَڢِے تَرٜىٰ دُواْمِنْ سُكَٰوُاْ عَݣُوتِنْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَرْ يَهْوٜىٰهْ دَغَ غِدَنْ عُواْبٜىٰدْ عٜىٰدُوامْ؞ عَكَ كُوَ كَٰوُاْ شِ ثِكِنْ ڢَضٍ ثِكِ سُواْسَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Haka Dawuda, da dattawan Isra'ilawa, da shugabannin dubu dubu, suka tafi da murna domin su ɗauko akwatin alkawarin Ubangiji daga gidan Obed-edom.