1 Chronicles 16:42 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Heman da Yedutun su ne da hakkin busa ƙahoni da kaɗa kuge da sauran kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin da ake rera waƙoƙi masu tsarki. ’Ya’yan Yedutun maza, su aka ba wa aikin tsaron ƙofa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
هٜىٰمَنْ دَ يٜىٰدُتُنْ نٜىٰ سُنَ لُورَ دَ كَكَكِ دَ كُغٜىٰ دَ كَايَنْ كَطٜىٰ كَطٜىٰ وَطَنْدَ عَكٜىٰ أَمْڢَانِ دَسُو دُواْمِنْ يِنْ وَاڧُواْڧِنْ يَبُواْ غَ اللَّهْ ؞ یَیَ مَظَا نَ يٜىٰدُتُنْ نٜىٰ عَكَسَا سُيِ غَادِنْ ڧُواْڢَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Heman da Yedutun suna lura da ƙaho, da kuge, da sauran kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin raira waƙoƙin yabo ga Allah. 'Ya'yan Yedutun, maza, su aka ba aikin tsaron ƙofa.