1 Chronicles 17:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na kasance tare da kai ko’ina ka tafi, na kuma yanke dukan abokan gābanka a gabanka. Yanzu zan sa sunanka kamar sunayen mutane mafi girma na duniya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكَ عِنْدَ كَتَڢِے إِنَ تَرٜىٰدَكَيْ، نَكُمَ كَوَرْدَ أَبُواْكَنْ غَابَنْكَ؞ ذَنْ كُوَسَا كَيِ سُونَ كَمَرْ وَطَنْدَ سُكَيِ سُونَ عَدُونِيَرْ نَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Na kuwa kasance tare da kai a duk inda ka tafi, na kuma hallaka maƙiyanka a gabanka. Zan sa ka shahara kamar waɗanda suka shahara a duniya.