1 Chronicles 17:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan kuma tanada wuri domin mutanena Isra’ila, zan kuma kafa su saboda za su kasance da gidan kansu ba kuwa za a ƙara damunsu ba. Mugayen mutane ba za su ƙara zaluntar su ba, yadda suka yi da farko
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَنْبَا مُتَنٜىٰنَ إِسْرَٰٓءِيلَ وُرِے سُذَوْنَ؞ ذَنْسَاسُ عِنْدَ ذَاسُيِ ذَمَنْ كَنْسُ بَاتَرٜىٰدَ أَنْدَمٜىٰسُبَ كُمَ؞ بَذَاعَ سَاكٜىٰ سَامِ مُوغَيٜىٰنْ مُتَنٜىٰ سُثُوثٜىٰسُ كَمَرْ دَا بَ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zan zaɓo wa jama'ata, wato Isra'ila, wuri, zan dasa su, su zauna a wuri na kansu, don kada a sāke damunsu, kada kuma masu mugunta su ƙara lalata su kamar dā,