1 Chronicles 18:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dawuda ya kame keken yaƙinsa dubu ɗaya, da mahayan kekunan yaƙi dubu bakwai da sojojin kafa guda dubu ashirin. Ya yayyanke dukan agaran dawakansa, amma ya bar dawakai da suka isa jan kekunan yaƙi ɗari.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَاوُدَ يَڨُوثٜىٰ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِنْسَ دُبُو طَيَ دَ مُتُمْ دُبُو بَݣَويْ مَاسُ هَوَنْ دَوَكِ دَ سُواْجُواْجِ دُبُو عَشِرِنْ؞ سَيْ دَاوُدَ يَغُرْغُنْتَ دُكَنْ دَوَكِ مَاسُ جَنْ كٜىٰكٜىٰنْ دُواْكِ، عَمَّا يَبَرْ غُدَا طَرِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Dawuda ya ƙwace karusai dubu (1,000), da mahayan dawakai dubu bakwai (7,000), da sojojin ƙasa dubu ashirin (20,000) daga gare shi. Dawuda kuma ya yanyanke agarar dawakan da suke jan karusai, amma ya bar waɗansu dawakai daga cikinsu waɗanda suka isa jan karusai ɗari.