1 Chronicles 18:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da Arameyawan Damaskus suka zo su taimaki Hadadezer sarkin Zoba, sai Dawuda ya bugi dubu ashirin da biyunsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ مُتَنٜىٰنْ سُورِيَ نَ دِمَشْڧُ سُكَذُواْ دُواْمِنْ سُتَيْمَكِ سَرْكِے هَدَدٜىٰظٜىٰرْ نَ ذُوابَ، دَاوُدَ يَكَشٜىٰ سُواْجُواْجِنْسُ غُدَا دُبُو عَشِرِنْ دَ بِيُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da Suriyawa daga Dimashƙu suka zo don su taimaki Hadadezer Sarkin Zoba, sai Dawuda ya karkashe mutum dubu ashirin da dubu biyu (22,000) daga cikin Suriyawan.