1 Chronicles 18:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya sa ƙungiyoyin sojoji a masarautar Arameyawan Damaskus. Arameyawan kuwa suka zama bayinsa, suka kuma kawo haraji. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a ko’ina da ya tafi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَكَڢَ بَرِكُواْكِنْ سُواْجُواْجِنْسَ أَ دِمَشْڧُ تَ سُورِيَ؞ مُتَنٜىٰنْ سُورِيَ كُوَ سُكَ ذَمَ بَايِنْ دَاوُدَ سُنَ كَٰوُاْ مَسَ هَرَاجِ؞ يَهْوٜىٰهْ يَكَنْ بَا دَاوُدَ نَصَرَا كُواْعِنَ دَ يَتَڢِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Dawuda ya sa ƙungiyoyin sojoji a Suriya ta Dimashƙu, Suriyawa kuma suka zama bayin Dawuda, suka riƙa kawo masa haraji. Ubangiji kuwa ya taimaki Dawuda duk inda ya tafi.