1 Chronicles 18:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Daga Teba da Kun, garuruwan da suke ƙarƙashin Hadadezer, Dawuda ya kwashe tagulla da yawa sosai, wanda Solomon ya yi amfani don yă yi Tekun tagulla, ginshiƙai da kuma kayayyakin tagulla dabam-dabam.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَاوُدَ يَكُمَ ݣُوشِ كَايَ دَيَوَ دَ عَكَيِ دَ تَغُلَّ دَغَ بِرَنٜىٰ عَڧَرْڧَشِنْ مُلْكٍ هَدَدٜىٰظٜىٰرْ، وَتُواْ تِبْهَتْ دَ كُنْ؞ دَغَ بَايَ سُلَيْمَٰنُ يَيِ أَمْڢَانِ دَ تَغُلَّرْ يَيِ ڧَتُوانْ ݣُونُوانْ ضُوَ وَنْدَ عَكٜىٰ كِرَنْسَ تٜىٰكُ دَ غِنْشِڧَيْ دَ كَايَيَّكِنْ هَيْكَلِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dawuda kuma ya kwaso tagulla mai yawan gaske daga Beta da Berotayi, biranen Hadadezer. Da su ne Sulemanu ya yi kwatarniya, da ginshiƙai, da kayayyakin Haikali.