1 Chronicles 19:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma Arameyawa suka gudu a gaban Isra’ila, mutanen Dawuda kuwa suka kashe masu hawan keken yaƙinsu dubu bakwai da sojojin ƙasa dubu arba’in. Ya kuma kashe Shobak shugaban mayaƙansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سُرِيَاوَا سُكَ غُدُ أَغَبَنْ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا؞ دَاوُدَ كُوَ يَكَشٜىٰ سُواْجُواْجِنْ سُورِيَ دُبُو بَݣَويْ مَاسُ كٜىٰكٜىٰنْ دُواْكِنْ يَاڧِ دَ سُواْجُواْجِ دُبُو أَرْبَعِنْ مَاسُ يَاڧِ عَڧَسَا؞ يَكُمَ كَشٜىٰ شُواْبَكْ شُوغَبَنْ سُواْجُواْجِنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
sai Suriyawa suka gudu a gaban Isra'ilawa, Dawuda ya karkashe Suriyawa, mutum dubu bakwai (7,000) masu karusai, da sojojin ƙasa dubu arba'in (40,000). Ya kuma kashe Shobak shugaban sojojin.