1 Chronicles 19:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dawuda ya yi tunani, “Zan nuna jinƙai ga Hanun ɗan Nahash, domin mahaifinsa ya nuna alheri gare ni.” Saboda haka Dawuda ya aika da tawaga don yă yi wa Hanun ta’aziyya game da mahaifinsa. Sa’ad da mutanen Dawuda suka iso wurin Hanun a ƙasar Ammonawa don su ta’azantar da shi,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ دَاوُدَ يَثٜىٰ «ذَنْ نُونَ أَلْحٜىٰرِ غَ هَنُنْ طَنْ نَهَشْ، غَمَا بَابَنْسَ يَنُونَ مِنِ أَلْحٜىٰرِ؞» دَاوُدَ يَعَيْكَ دَ وَكِلَنْسَ ذُوَا وُرِنْ هَنُنْ دُواْمِنْ سُغَيْشٜىٰشِ عَكَنْ مُتُوَرْ بَابَنْسَ؞ سَيْ وَكِلَيْ سُكَ تَڢِے وُرِنْ هَنُنْ عَڧَسَرْ أَمُّوانْ دُواْمِنْ سُغَيْشٜىٰشِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Dawuda ya ce, “Zan nuna alheri ga Hanun ɗan Nahash, gama tsohonsa ya nuna mini alheri.” Don haka Dawuda ya aiki manzanni su yi wa Hanun ta'aziyyar rasuwar tsohonsa. Fādawan Dawuda suka zo ƙasar Ammon wurin Hanun, domin su yi masa ta'aziyya.