1 Chronicles 19:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
sai manyan Ammonawa suka ce wa Hanun, “Kana tsammani Dawuda yana girmama mahaifinka ne da ya aika mutanen nan wurinka su ta’azantar da kai? Ba mutanensa sun zo ne su bincika su kuma leƙi ƙasar su tumɓuke ta ba?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا شُوغَبَنِّنْ أَمُّوانْ سُكَثٜىٰ وَ هَنُنْ «كَنَ ڟَمَّنِ دَاوُدَ يَنَ غِرْمَمَ بَابَنْكَ نٜىٰ دَ يَعَيْكِ مَاسُ حِدِمَرْسَ سُغَيْشٜىٰكَ عَكَنْ مُتُوَرْ بَابَنْكَ؟ أَيْ سُنْ ذُواْ نٜىٰ دُواْمِنْ سُدُوبِے أَسِيرِنْ ڧَسَرْ، سُبِنْثِكٜىٰتَ، سُثِتَ دَيَاڧِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma hakiman Ammonawa suka ce wa Hanun, “Kana tsammani Dawuda yana girmama tsohonka ne da ya aiko manzanni su yi maka ta'aziyya? Fādawansa sun zo wurinka ne don su leƙi asirin ƙasar, su bincike ta, su ci ta da yaƙi.”