1 Chronicles 19:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da Ammonawa suka gane cewa sun zama abin wurin a kafan hancin Dawuda, Hanun da Ammonawa suka aika da talenti dubu na azurfa don su yi haya da kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi daga Aram-Naharayim, Aram Ma’aka da Zoba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
لُواْكَثِنْ دَ أَمُّواْنَاوَا سُكَ غَانٜىٰ ثٜىٰوَ سُنْ سَا دَاوُدَ يَڧِ جِنِنْسُ، سَيْ سَرْكِے هَنُنْ دَ أَمُّواْنَاوَا سُكَ عَيْكَ دَ كِلُواْ دُبُو تَلَاتِنْ دَ حُطُ نَأَظُرْڢَا دُواْمِنْ سُيِ هَيَرْ كٜىٰكُنَنْ دُواْكِ دَ سُواْجُواْجِ مَاسُ هَوَنْ دَوَكِ دَغَ يَنْكِنْ مٜىٰسُواْڢُواْتَمِيَ دَغَ كُمَ مَعَكَ دَ ذُوابَ تَڧَسَرْ سُورِيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da Ammonawa suka ga sun mai da kansu abin ƙi ga Dawuda, sai Hanun da Ammonawa suka aika da talanti dubu (1,000) na azurfa don su yi ijara da karusai da mahayan dawakai daga Mesofotamiya, da jihohin Ma'aka ta Suriya, da Zoba.