1 Chronicles 2:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kaleb ɗan Hezron ya haifi yara ta wurin matarsa Azuba (da kuma ta wurin Yeriyot). Waɗannan su ne ’ya’yan Azuba maza. Yesher, Shobab da Ardon.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَلٜىٰبْ طَنْ هٜىٰظْرُوانْ يَنَدَ یَیَ تَرٜىٰدَ مَاتَرْسَ أَظُبَ؞ يَنَ كُمَ دَ یَیَ تَرٜىٰدَ يٜىٰرِيُواتْ؞ سُونَيٜىٰنْ یَیَ مَظَا نَاتَ سُونٜىٰ، يٜىٰشٜىٰرْ دَ شُواْبَبْ دَ أَرْدُوانْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Azuba, matar Kalibu ɗan Hesruna ta haifa masa 'ya'ya maza. Matarsa Yeriyot kuma ta haifi 'ya'ya maza, su ne Yesher, da Shobab, da Ardon.