1 Chronicles 20:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dawuda ya ɗauki rawani daga kan sarkinsu, nauyinsa ya kai talenti na zinariya, aka kuma yi masa ado da duwatsu masu daraja, sai Dawuda kuwa ya sa a kansa. Ya kuma kwashi ganima mai yawa daga birnin
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَاوُدَ يَسَا عَكَ ثِرٜىٰ هُولَرْ مُلْكِ دَغَ كَنْ سَرْكِنْسُ، عَكَسَا مَسَ عَكَيْ؞ نَوْيِنْ ظِينَارِيَ تَهُولَرْ سَرْكِنْ كُوَ يَكَيْ وَجٜىٰنْ كِلُواْ تَلَاتِنْ دَ حُطُ؞ هُولَرْ مُلْكِ كُمَ يَنَدَ أَدُوانْ دُوَڟُو مَاسُ دَرَجَ أَجِكِنْسَ؞ سَعَنً دَاوُدَ يَݣُوسُواْ كَايَنْدَ يَڨُوثٜىٰ عَيَاڧِ دَيَوَ دَغَ ثِكِنْ بِرْنِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Dawuda ya ciro kambi daga kan sarkinsu, sai ya iske nauyinsa talanti ɗaya na zinariya ne, akwai kuma duwatsu masu daraja a cikinsa. Dawuda ya sa kambin a kansa. Ya kwaso ganima da yawa a birnin.