1 Chronicles 20:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yaƙi kuma ya sāke tashi tsakanin Isra’ilawa da Filistiyawa, Elhanan ɗan Yayir ya kashe Lahmi ɗan’uwan Goliyat mutumin Gat, wanda yake riƙe da māshi mai sandan masaƙa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَكَ سَاكٜىٰيِنْ يَاڧِ دَ ڢِلِسْتِيَاوَا، سَيْ عٜىٰلْهَنَنْ طَنْ يَايِرْ يَكَشٜىٰ لَمِ طَنْعُوَنْ جَالُوتَ وَنْدَ يَڢِتُواْ دَغَ غَتْ، كُمَ غِرْمَنْ سَنْدَنْ مَاشِنْسَ يَيِ كَمَ دَ تَٻَرْيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yaƙi kuma ya sake tashi tsakanin Isra'ilawa da Filistiyawa, sai Elhanan ɗan Yayir, ya kashe Lahmi ɗan'uwan Goliyat daga Gat, wanda yake gorar mashinsa ta yi ya dirkar masaƙa.