1 Chronicles 21:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma Yowab ya amsa ya ce, “ Ubangiji ya riɓaɓɓanya mayaƙansa fiye da sau ɗari. Ranka yă daɗe sarki, dukansu ba bayin shugabana ba ne? Me ya sa ranka yă daɗe yake so yă yi haka? Me zai sa ka kawo laifi a kan Isra’ila?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا يُواْوَبْ يَثٜىٰ وَسَرْكِے «رَنْكَيَدَطٜىٰ، سَرْكِے! بَرِ يَهْوٜىٰهْ يَڧَارَ مُتَنٜىٰنْسَ سَوْ طَرِے بِسَ كَنْ يَدَّ سُكٜىٰ عَيَنْظُ! يَا سَرْكِے، بَ دُكَنْسُ نَاكَ بَنٜىٰ؟ دُواْمِنْ مٜىٰنٜىٰنٜىٰ ذَاكَسُواْ مُيِ وَنَّنْ أَبُ؟ دُواْمِنْ مٜىٰ ذَاكَ جَٰوُاْوَ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ أَبِنْدَ ذَيْسَا سُيِ لَيْڢِے؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma Yowab ya ce, “Ubangiji ya riɓaɓɓanya yawan jama'arsa har sau ɗari bisa kan yadda suke a yanzu! Ranka ya daɗe, ya sarki, ashe, dukkansu ba naka ba ne? Me zai sa shugabana ya so a yi haka? Me zai sa ya zama sanadin tuntuɓe ga mutanen Isra'ila?”