1 Chronicles 21:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yowab ya ba labarin yawan mayaƙan wa Dawuda. A cikin Isra’ila akwai mutum miliyon da dubu ɗari ɗaya waɗanda za su iya riƙe takobi, haɗe da dubu ɗari huɗu da saba’in a Yahuda.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يُواْوَبْ يَبَا دَاوُدَ لِسَّڢِنْ يَوَنْ مُتَنٜىٰنْ؞ أَ دُكَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ أَݣَويْ مَظَا مِلِيَنْ طَيَ دَ دُبُو طَرِے وَطَنْدَ سُكَ إِسَ يَاڧِ؞ أَ يَنْكِنْ يَهُودَ أَݣَويْ مَظَا دُبُو طَرِے حُطُ دَ دُبُو سَبَعِنْ دَ سُكَ إِسَ يَاڧِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yowab ya kawo wa Dawuda adadin yawan mutanen. Jimillar dukan Isra'ila zambar dubu ne da dubu ɗari (1,100,000) waɗanda za su iya yaƙi. Jimillar mutanen Yahuza kuwa dubu ɗari huɗu da dubu saba'in ne (470,000) waɗanda suka isa zuwa yaƙi.