1 Chronicles 22:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shi ne wanda zai gina gida saboda Sunana. Zai zama ɗana, ni kuma zan zama mahaifinsa. Zan kafa kujerar sarautarsa a bisa Isra’ila har abada.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَيْ كُمَ غِنَاوَا يَهْوٜىٰهْ غِدَا دُواْمِنْ طَوْكَكَرْ سُونَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ يَهْوٜىٰهْ يَثٜىٰ، ‹ذَيْ ذَمَ طَا أَغَرٜىٰنِ، نِے كُمَ إِنْ ذَمَ بَابَ أَغَرٜىٰشِ، ذَنْ كُمَ كَڢَ كُجٜىٰرَرْ مُلْكِنْسَ حَرْ أَبَدَا؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Shi zai gina Haikali saboda sunana. Zai zama ɗana, ni kuwa zan zama uba a gare shi, zan kafa gadon sarautarsa a Isra'ila har abada.’