1 Chronicles 22:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ta haka za ka yi nasara in ka mai da hankali ga kiyaye ƙa’idodi da dokokin da Ubangiji ya ba wa Musa saboda Isra’ila. Ka yi ƙarfin hali ka kuma ƙarfafa. Kada ka ji tsoro ko ka fid da zuciya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاكَ يَلْوَتَ عِدَنْ كَيِ بِيَيَّ دَ ڧَٰعِدُواْدِ دَ عُمَرْنَيْ وَطَنْدَ يَهْوٜىٰهْ يَعُمَرْثِ مُوسَٰى غَمٜىٰدَ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا؞ كَڧَرْڢَڢَ، كَيِ ڧَرْڢِنْ حَلِ؞ كَدَ كَجِڟُواْرُواْ، كَدَ كَڢِدَّ ذُوثِيَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za ka arzuta idan ka kula ka kiyaye dokoki da ka'idodi da Ubangiji ya umarci Musa saboda Isra'ila. Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karaya.