1 Chronicles 22:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dawuda kuwa ya umarta a tattara baƙin da suke zama a Isra’ila, daga cikinsu ya sa masu farfasa duwatsu don su shirya duwatsun da aka sassaƙa saboda ginin gidan Allah.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے دَاوُدَ يَبَادَ عُمَرْنِ ثٜىٰوَ عَتَتَّارَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ دَسُكٜىٰ بَ یَنْ ڧَسَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ بَ؞ دَغَ ثِكِنْسُ يَسَا سُكَ سَسَّڧَ دُوَڟُو سُڠَرَ دُوَڟُو مَاسُ ݣَنْ غَنِ دُواْمِنْ غِنِنْ غِدَنْ اللَّهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dawuda kuwa ya umarta a tattaro dukan baƙin da suke a ƙasar Isra'ila. Ya sa waɗansu su farfasa duwatsu, su sassaƙe duwatsun domin ginin Haikalin Allah.