1 Chronicles 23:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Waɗannan ne zuriyar Lawi bisa ga iyalansu, kawunan iyalai kamar yadda aka rubuta su a ƙarƙashin sunayensu aka kuma ƙirga kowa, wato, masu aikin da suke ’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye waɗanda suka yi hidima a cikin haikalin Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَطَنَّنْ نٜىٰ ذُرِيَرْ لَوِ بِسَغَ دَنْغِنْسُ، وَتُواْ شُوغَبَنِّنْ غِدَاجٜىٰنْ كَاكَنِّنْسُ دَ عَكَ رُبُوتَ سُونَيٜىٰنْسُ طَيَ طَيَ دَغَ مَيْ شٜىٰكَرَا عَشِرِنْ ذُوَا سَمَ؞ سُونٜىٰ ذَاسُيِ عَيْكِنْ حِدِمَ أَ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗannan su ne 'ya'yan Lawi, maza, bisa ga gidajen kakanninsu, wato su ne shugabannin da aka rubuta sunayensu ɗaya ɗaya daga mai shekara ashirin da haihuwa zuwa sama. Su ne za su yi hidima a cikin Haikalin Ubangiji.