1 Chronicles 23:29 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Su ne za su lura da burodin da aka ajiye a tebur, lallausan gari don hadaya ta gari, waina marar yisti, toyawa da kwaɓawa, da kuma dukan awon yawa da kuma girman abubuwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُونٜىٰ سُكٜىٰ دَ حَكِّنْ شِمْڢِطَا غُرَاسَرْ دَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ عَكَنْ تٜىٰبُرِنْسَ دَ غَارِ مَيْ لَوْشِ دُواْمِنْ هَدَايَرْ حَڟِ دَ بِسْكِتْ مَرَرْ يِسْتِ دَ كُمَ هَدَايُنْ أَبِنْدَ عَكَ تُواْيَ دَ نَأَبِنْدَ عَكَ ݣُوٻَ دَ أَبُبُوَنْ عَوْنَ نَكُواْوَنٜىٰ إِرِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za su kuma taimaka wajen gurasar ajiyewa, da lallausan gari na hadaya ta gari, da waina marar yisti, da abin da akan toya, da abin da akan kwaɓa, da ma'aunan nauyi da na girma.