1 Chronicles 23:32 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A haka kuwa Lawiyawa suka yi ayyukansu don Tentin Sujada, don Wuri Mai Tsarki da kuma a ƙarƙashin ’yan’uwansu zuriyar Haruna, saboda hidimar haikalin Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ لَوِيَاوَا سُكَيِ حِدِمَرْسُ نَتٜىٰنْتِنْ كَسَنْثٜىٰوَرْ يَهْوٜىٰهْ دَ وُرِے مَڢِے ڟَرْكِے دَ كُمَ حِدِمَرْ سُجَّدَ أَ هَيْكَلِ عَڧَرْڧَشِنْ یَنْعُوَنْسُ دَنْ‌غِنْ هَٰرُونَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Su ne za su riƙa lura da alfarwa ta sujada, da Wuri Mai Tsarki, za su kuma taimaki 'ya'yan Haruna, maza, 'yan'uwansu, da yin hidimar Haikalin Ubangiji.