1 Chronicles 24:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shemahiya ɗan Netanel, wani Balawe ne marubuci, ya rubuta sunayensu a gaban sarki da kuma a gaban manyan ma’aikata. Zadok firist, Ahimelek ɗan Abiyatar da kuma kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa, iyali guda daga Eleyazar, guda kuma daga Itamar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
شٜىٰمَيَ طَنْ نٜىٰتَنٜىٰلْ مُتُمِنْ لَوِ نٜىٰ مَرُبُوثِ؞ يَرُبُوتَ سُونَيٜىٰنْسُ أَغَبَنْ سَرْكِے دَ دَتَّاوَنْسَ، وَتُواْ ظَدُواكْ ڢِرِسْتِ دَ أَهِمٜىٰلٜىٰكْ طَنْ أَبِيَتَرْ دَ شُوغَبَنِّنْ غِدَاجٜىٰنْ كَاكَنِّنْ ڢِرِسْتُواْثِے دَ نَ لَوِيَاوَا؞ عَكَ ذَاٻِ عِيَلِ غُدَا دَغَ دَنْغِنْ عٜىٰلٜىٰيَظَرْ دَ عِيَلِ غُدَا كُمَ دَغَ دَنْغِنْ عِتَمَرْ دُواْمِنْ ڟَارِنْ عَيْكِنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Shemaiya, ɗan Netanel marubuci, Balawe, ya rubuta su a gaban sarki da shugabanni, da Zadok firist, da Ahimelek ɗan Abiyata, da shugabannin gidajen kakannin firistoci, da Lawiyawa. Aka ɗauki gida guda daga gidajen kakannin Ele'azara, aka kuma ɗauki ɗaya daga gidajen kakannin Itamar.