1 Chronicles 25:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Game da Yedutun kuwa, daga ’ya’yansa maza. Gedaliya, Zeri, Yeshahiya, Shimeyi, Hashabiya da Mattitiya, su shida ne duka, a ƙarƙashin kulawar mahaifinsu Yedutun, wanda ya yi annabci, yana amfani da garaya a yin godiya da yabon Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَغَ یَیَ مَظَا نَ يٜىٰدُتُنْ، أَݣَويْ غٜىٰدَلِيَ دَ ظٜىٰرِ دَ يٜىٰشَيَ دَ شِمٜىٰيِ دَ هَشَبِيَ دَ مَتِّتِيَ، دُكَنْسُ شِدَ؞ سُنْيِ حِدِمَ ڧَرْڧَشِنْ جَغُواْرَنْثِنْ بَابَنْسُ وَنْدَ يَمُواْضِ مُواْلُواْ يَنَ أَنَّبْثِ دَ غُواْدِيَ دَ يَبُواْ غَ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Na wajen Yedutun, su ne 'ya'yan Yedutun, maza, wato Gedaliya, da Zeri, da Yeshaya, da Shimai, da Hashabiya, da Mattitiya, su shida ne. Mahaifinsu Yedutun shi ne yake bi da su, shi ne kuma mai raira waƙoƙi da garaya domin godiya da yabon Ubangiji.