1 Chronicles 26:30 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Daga zuriyar Hebron, Hashabiya da danginsa, su jarumawa dubu ɗaya da ɗari bakwai ne, su suke lura da Isra’ila yamma da Urdun don dukan aikin Ubangiji da kuma hidimar sarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَغَ دَنْغِنْ هٜىٰبْرُوانْ، أَنْذَاٻِ هَشَبِيَ دَ یَنْعُوَنْسَ دُواْمِنْ سُيِ عَيْكِنْ يَهْوٜىٰهْ دَ نَسَرْكِے عَيَنْكِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ يَمَّ غَ كُواْغِنْ يُواْدَنْ؞ مُتَنٜىٰ دُبُو دَ طَرِے بَݣَويْ مَاسُ عِيَ عَيْكِ سُواْسَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Hashabiya da 'yan'uwansu, su dubu da ɗari bakwai (1,700), gwanaye ne, daga zuriyar Hebron, su ne suke lura da Isra'ilawan yamma da Urdun a kan aikin Ubangiji da na sarki.