1 Chronicles 26:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ɗaukan waɗannan zuriyar Obed-Edom ne; su da ’ya’yansu maza da danginsu, jarumawa ne masu ƙarfin yin aiki. Zuriyar Obed-Edom, mutum 62 ne duka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكَنْ وَطَنَّنْ دَنْ‌غِنْ عُواْبٜىٰدْ عٜىٰدُوامْ نٜىٰ؞ سُو دَ یَیَنْسُ مَظَا دَ یَنْعُوَنْسُ سُنْ عِيَ عَيْكِنْ دَ عَكَبَاسُ، كُمَ سُنَدَ ڧَرْڢِنْ دَ ذَاسُيِ عَيْكِنْ؞ مَاسُ عَيْكِ دَغَ دَنْ‌غِنْ عُواْبٜىٰدْ عٜىٰدُوامْ، مُتَنٜىٰ سِتِّنْ دَ بِيُ نٜىٰ دُكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗannan duka iyalin Obed-edom ne. Su da 'ya'yansu maza da 'yan'uwansu suna da ƙarfi da gwaninta na yin aiki. Su sittin da biyu ne daga wajen Obed-edom.