1 Chronicles 27:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wannan shi ne jerin Isra’ilawa, kawunan iyalai, shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da manyan ma’aikatansu, waɗanda suka yi wa sarki hidima a dukan abin da ya shafi ɓangarorin mayaƙan da suke aiki wata-wata a dukan shekara. Kowane sashe yana da mutane 24,000.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا لِسَّڢِنْ سُونَيٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَاوَنْ دَ سُكَيِ وَسَرْكِے حِدِمَ أَ عَيْكِنْ سُواْجَ؞ عَثِكِنْسُ أَݣَويْ شُوغَبَنِّنْ غِدَاجٜىٰنْ كَاكَنِّ دَ شُوغَبَنِّنْ سُواْجُواْجِ دُبُو دُبُو دَ شُوغَبَنِّنْ سُواْجُواْجِ طَرِے طَرِے دَ سَوْرَنْ مَنْيَنْ سُواْجُواْجِ؞ كُواْوَثٜىٰ ڧُنْ‌غِيَ تَنَدَ مُتَنٜىٰ دُبُو عَشِرِنْ دَ حُطُ؞ كُواْوَثٜىٰ ڧُنْ‌غِيَرْ سُواْجَ تَكَنْيِ عَيْكِ وَتَا طَيَ عَكُواْوَثٜىٰ شٜىٰكَرَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga lissafin kawunan iyalin Isra'ilawa, da shugabannin dangi, da jama'a masu gudanar da ayyukan mulki. A kowane wata akan sauya aikin ƙungiyar mutum dubu ashirin da dubu huɗu (24,000), a ƙarƙashin shugaban aiki na wannan wata. Kowane wata akan sauya, wata ƙungiya ta kama aiki.