1 Chronicles 28:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dawuda ya sa aka kira dukan shugabannin Isra’ila su taru a Urushalima, shugabannin kabilu, manyan hafsoshin ɓangarorin hidimar sarki, manyan hafsoshin dubu-dubu da manyan hafsoshin ɗari-ɗari, da kuma shugabanni masu lura da dukan mallaka da dabbobin da suke na sarki da kuma ’ya’yansa maza, tare da fadawa, jarumawa da kuma dukan mayaƙa masu kwarjini.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَاوُدَ يَسَا دُكَنْ شُوغَبَنِّنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَ تَارُ أَ عُرُوشَلِيمَ؞ ثِكِنْسُ أَݣَويْ شُوغَبَنِّنْ ظُرِيُواْيِ دَ شُوغَبَنِّنْ ڧُنْ‌غِيُواْيِنْ دَسُكٜىٰيِ وَسَرْكِے حِدِمَ دَ شُوغَبَنِّنْ سُواْجُواْجِ دُبُو دُبُو دَ نَطَرِے طَرِے دَ مَاسُ لُورَ دَ دُكَنْ كَايَ دَ دَبُّواْبِنْ سَرْكِے دَ نَیَیَنْسَ، تَرٜىٰدَ دَتَّاوَنْسَ دَ مَنْيَنْ مُتَنٜىٰنْ ڧَسَرْدَ دُكَنْ مَنْيَنْ سُواْجُواْجِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dawuda ya yi umarni a tara dukan shugabannin Isra'ila, da shugabannin kabilai, da shugabannin ƙungiyoyin da suke bauta wa sarki, da shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da masu lura da dukan dukiya da dabbobin sarki, da na 'ya'yansa, da fādawa, da manyan sojoji, da jarumawa, a Urushalima.