1 Chronicles 28:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
da kuma yawan tacecciyar zinariya don bagaden turare. Ya kuma ba shi tsari don keken yaƙi, wato, kerubobin zinariyar da suka miƙe fikafikansu suka inuwantar da akwatin alkawarin Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ يَوَنْ ظِينَارِيَ ظَلَّ وَنْدَ ذَاعَيِ أَمْڢَانِ دَ عِتَ دُواْمِنْ بَغَدٜىٰنْ ڧُواْنَ تُرَارٜىٰ؞ يَكُمَ بَا سُلَيْمَٰنُ ڟَارِنْ كٜىٰكٜىٰنْ دُواْكِ نَظِينَارِيَ دَ نَحَلِتُّو مَاسُ ڢِكَڢِكَنْ دَ ذَاسُ رُڢٜىٰ عَݣُوتِنْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ نَ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
da yawan zinariya tsantsa wadda za a yi bagaden ƙona turare da ita. Ya kuma ba shi tsarin zinariya ta kerubobin da za su miƙe fikafikansu su rufe akwatin alkawari na Ubangiji.