1 Chronicles 28:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarki Dawuda ya miƙe tsaye ya ce, “Ku saurare ni, ’yan’uwana da kuma mutanena. Na yi niyya in gina gida a matsayin wurin hutu domin akwatin alkawarin Ubangiji, domin zatin Allahnmu, na kuma yi shiri don in gina shi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَاوُدَ يَتَاشِ ڟَيٜىٰ أَغَبَنْسُ يَثٜىٰ «كُجِنِ، يَا كُو یَنْعُوَنَ دَ مُتَنٜىٰنَ؞ نَا طَوْكَ أَ ذُوثِيَاتَ ذَنْ غِنَا غِدَنْ هُوتَوَا دُواْمِنْ عَݣُوتِنْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَرْ يَهْوٜىٰهْ ، كُمَ وُرِنْ سَا ڧَڢَرْ اللَّهْ نْمُ؞ نَارِغَا نَا يِشِرِ دُواْمِنْ غِنِنْ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sarki Dawuda fa ya miƙe tsaye, ya ce, “Ku saurare ni, ku 'yan'uwana, da jama'ata. Na yi niyya a zuciyata in gina wa akwatin alkawari na Ubangiji wurin hutawa, da wurin zaman zatin Allah. Na riga na yi shiri domin ginin,