1 Chronicles 28:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Duk da haka Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya zaɓe ni daga dukan iyalina don in zama sarki bisa Isra’ila har abada. Ya zaɓi Yahuda a matsayin shugaba, kuma daga gidan Yahuda ya zaɓi iyalina, daga ’ya’yan mahaifina maza kuwa ya gamsu ya mai da ni sarki bisa dukan Isra’ila.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«عَمَّا دُكْدَهَكَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ يَذَاٻٜىٰنِ دَغَ یَیَنْ بَابَنَ دُواْمِنْ إِنْ ذَمَ سَرْكِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ حَرْ أَبَدَا؞ غَمَا يَذَاٻِ كَكَنْمُ يَهُودَ يَذَمَ شُوغَبَا ثِكِنْ ظُرِيُواْيِنْ يَهُودَ؞ عَثِكِنْ یَیَنْ يَهُودَ كُمَ يَذَاٻِ بَابَنَ؞ عَثِكِنْ یَیَنْ بَابَنَ كُمَ يَذَاٻٜىٰنِ إِنْ ذَمَ سَرْكِے عَكَنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Duk da haka Ubangiji Allah na Isra'ila ya zaɓe ni da zuriyata daga cikin gidan mahaifina, in zama Sarkin Isra'ilawa har abada. Gama shi ya zaɓi Yahuza ya zama shugaba. Daga cikin gidan Yahuza kakana, da kuma daga cikin 'ya'yan mahaifina, maza, ya ji daɗina har ya naɗa ni sarkin dukan Isra'ila.