1 Chronicles 29:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka ci suka sha da farin ciki mai girma a gaban Ubangiji a wannan rana. Sa’an nan suka yarda da Solomon ɗan Dawuda a matsayin sarki sau na biyu, suka shafe shi a gaban Ubangiji don yă zama mai mulki, Zadok kuwa ya zama firist.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ رَانَرْ نَنْ كُواْوَ يَثِ يَشَا تَرٜىٰدَ مُرْنَ مَيْ يَوَ غَ يَهْوٜىٰهْ ؞ سَيْ سُكَسَاكٜىٰ تَبَّتَرْ دَ سُلَيْمَٰنُ طَنْ دَاوُدَ سَرْكِے سَوْ نَبِيُ؞ سُكَ ظُبَ مَسَ مَنْ كٜىٰٻٜىٰوَ نَنَطَ شِ سَرْكِے أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ حَكَ مَا عَكَ ظُبَ وَ ظَدُواكْ مَنْ كٜىٰٻٜىٰوَ دُواْمِنْ عَكٜىٰٻٜىٰشِ ڢِرِسْتِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai suka ci, suka sha, suka yi murna a gaban Ubangiji a wannan rana. Sai suka sake shelar naɗin Sulemanu ɗan Dawuda sarki, a karo na biyu, suka shafa masa man keɓewa domin ya zama mai mulki na Ubangiji, Zadok kuwa shi ne firist.