1 Chronicles 3:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Waɗannan su ne ’ya’yan Dawuda maza da aka haifa masa a Hebron. Ɗan farinsa shi ne Amnon ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel; na biyun, Daniyel ɗan Abigiyel mutuniyar Karmel;
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَطَنَّنْ سُونٜىٰ یَیَ مَذَنْ دَ عَكَ حَيْڢَ وَ دَاوُدَ أَ هٜىٰبْرُوانْ؞ طَا نَڢَارِ شِينٜىٰ أَمْنُوانْ، وَنْدَ مَامَرْسَ ثٜىٰ أَهِنُواْوَمْ دَغَ يٜىٰظِرٜىٰيٜىٰلْ؞ نَبِيُنْ شِينٜىٰ دَانِيٜىٰلْ وَنْدَ مَامَرْسَ ثٜىٰ أَبِغِيٜىٰلْ دَغَ كَرْمٜىٰلْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗannan su ne 'ya'yan Dawuda, maza, waɗanda aka haifa masa a Hebron. Amnon wanda Ahinowam Bayezreyeliya ta haifa masa. Kileyab wanda Abigail Bakarmeliya ta haifa masa. Absalom ɗan Ma'aka 'yar Talmai, Sarkin Geshur. Adonaija ɗan Haggit. Shefatiya wanda Abital ta haifa. Itireyam wanda Egla ta haifa.