1 Chronicles 4:41 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutanen da aka jera sunayensu sun zo ne a zamanin Hezekiya sarkin Yahuda. Suka yaƙi mutanen Ham a wuraren zamansu, haka kuma suka yi da Meyunawa da suke can, suka hallaka su ƙaƙaf, yadda yake har yă zuwa yau. Sa’an nan suka zauna a wurin, gama akwai makiyaya domin garkunansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ ذُرِيَرْ سِمٜىٰيُوانْ دَ عَكَ بَادَ سُونَيٜىٰنْسُ، سُونٜىٰ سُكَذُواْ أَ زَامَانِنْ سَرْكِے هٜىٰزٜىٰكِيَ نَ يَهُودَ، سُكَ ڢَاطَ وَمُتَنٜىٰنْ هَمْ دَ يَاڧِ سُكَ ڨُوثٜىٰ وُرَارٜىٰنْ ذَمَنْسُ دَ نَ مٜىٰيُنِيَاوَنْ دَسُكٜىٰ ذَمَ أَوُرِنْ؞ سُكَ كَوَرْ دَسُو غَبَاطَيَ أَوُرِنْ، كَمَرْ يَدَّ يَكٜىٰ هَرْوَيَوْ؞ سَعَنً سُكَ ذَوْنَ عَڧَسَرْ سَبُواْدَ أَݣَويْ عَبِنْثِ مَيْ يَوَ أَوُرِنْ دُواْمِنْ دَبُّواْبِنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗannan da aka lasafta sunayensu, su ne suka zo a kwanakin Hezekiya Sarkin Yahuza, suka fāɗa wa alfarwai da bukkoki waɗanda suka tarar a can, suka hallaka su sarai, sa'an nan suka maye wurinsu saboda akwai makiyaya domin garkunansu a wurin.