1 Chronicles 5:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutanen Ruben, mutanen Gad da rabin kabilar Manasse sun kasance da mutane 44,760 shiryayyu don aikin soja, jarumawan da za su iya riƙe garkuwa da takobi, waɗanda suke iya yin amfani da baka, waɗanda kuma aka horar don yaƙi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذُرِيَرْ رَعُبَيْنُ دَ تَ غَدْ دَ رَبِنْ ذُرِيَرْ مَنَسّٜىٰ مَذَوْنَنْ غَبَسْ، سُنَدَ سُواْجُواْجِ دُبُو أَرْبَعِنْ دَ حُطُ دَ طَرِے بَݣَويْ دَ سِتِّنْ وَطَنْدَ سُكَ ڠُونِنْتَ وَجٜىٰنْ أَمْڢَانِ دَ غَرْكُوَ دَ تَكُواْبِے دَ كُمَ بَكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
'Ya'yan Ra'ubainu, maza, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa suna da jarumawa masu riƙon garkuwa da takobi, masu harbi kuma da baka. Gwanayen yaƙi ne, su dubu arba'in da huɗu, da ɗari bakwai da sittin ne (44,760).