1 Chronicles 6:77 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutanen Merari (sauran Lawiyawan) suka sami waɗannan. Daga kabilar Zebulun suka sami Yokneyam, Karta, Rimmon da Tabor, tare da wuraren kiwonsu;
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَوْرَنْ عِيَلَنْ ذُرِيَرْ مٜىٰرَرِ أَنْبَاسُ وَطَنَّنْ غَرُرُوَ، وَتُواْ دَغَ يَنْكِنْ ذُرِيَرْ ظٜىٰبُلُنْ أَݣَويْ غَرُضُوً رِمُّوانْ دَ تَبُوارْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Daga na kabilar Zabaluna, an ba sauran Lawiyawa, wato 'ya'yan Merari, maza, Rimmon duk da makiyayarta, da Tabor duk da makiyayarta.