1 Chronicles 7:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
’Ya’yan Tola maza su ne, Uzzi, Refahiya, Yeriyel, Ibsam da Sama’ila, su ne kuma kawunan iyalansu. A zamanin mulkin Dawuda, an rubuta zuriyar Tola a matsayin mayaƙa a cikin tarihinsu, sun kai 22,600.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
یَیَ مَظَا نَ تُواْلَ سُونٜىٰ، عُظِّ دَ رٜىٰڢَيَ دَ يٜىٰرِيٜىٰلْ دَ يَمَيْ دَ إِبْسَمْ دَ سَمَٰعِيلَ؞ دُكَنْسُ شُوغَبَنِّنْ عِيَلَنْ دَنْغِنْ تُواْلَ نٜىٰ دَ كُمَ سُواْجُواْجِ مَاسُ عِيَ يَاڧِ؞ أَ لُواْكَثِنْ مُلْكٍ سَرْكِے دَاوُدَ يَوَنْ ذُرِيَرْسُ يَكَيْ مَظَا دُبُو عَشِرِنْ دَ بِيُ دَ طَرِے شِدَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
'Ya'yan Tola, maza, su ne Uzzi, da Refaya, da Yeriyel, da Yamai, da Ibsam, da Sama'ila, su ne shugabannin gidajen kakanninsu. 'Ya'yan Tola kuwa manyan mayaƙa ne a zamaninsu. Yawansu a zamanin Dawuda, su dubu ashirin da biyu ne da ɗari shida (22,600).