1 Chronicles 7:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan ya sāke kwana da matarsa, sai ta yi ciki ta haifi ɗa. Ya ba shi suna Beriya, saboda masifar da ta auko a cikin iyalinsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِڢْرَيِمْ يَݣُونَ دَ مَاتَرْسَ، تَايِثِكِ تَحَيْڢِ طَا، عَكَ بَاشِ سُونَ بٜىٰرِيَ، غَمَا مَسِيڢَ تَڢَاطُواْ أَغِدَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan ya shiga wurin matarsa, ta kuwa sami juna biyu, ta haifi ɗa, ya raɗa masa suna Beriya saboda masifar da ta auko wa gidansa.